Labarai

Amarya ta caccaka wa mijinta wuka a karo na 3 da take yunkurin kashe shi

Amaryar da ake zargi dake zama a jihar Kano ta caccakawa mijinta wuka a ciki bayan zamansu na watanni 6.

An zargi Fatima Musa da caccakawa mijinta mai suna Sa’eed Muhammad Hussain wukar a cikinshi mai dauke da guba, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.

Bisa bincike, DABO FM ta gano yanzu haka Sa’eed Muhammad yana kwance a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano inda yake karbar kulawa daga wajen likitoci a yanayin yanzu.

A nasu bangaren, yan uwan Fatima Musa sun hallara a asibitin Mallam Aminu Kano inda suka bayyana cewa “Yar su bazata taba aikata wannan mummunan aiki ba.”

Sai dai DABO FM ta binciko cewa wannan ne karo na 3 da Fatima Musa tayi yunkurin hallaka mijinnata a kasa da watanni 6 na aurensu kamar yadda yan uwanshi suka bayyana mana.

Fatima Musa Hamza, dalibace da take karatun Law a jami’ar Bayero dake jihar Kano.

Yanzu haka dai Fatima tana tsare a hannun rundunar ‘yan sandan jihar Kano.

DABO FM ta tattauna ta wayar tarho da wasu daga cikin abokan karatun ta wacce ta bukaci mu sakaya sunanta inda ta bayyana mana kadan daga cikin abinda ta sani game da batun.

“Hanan kawar muce tin muna aji daya a BUK, mace ta nitsattsiya mai dattaku.”

“Kwana biyu munga bata zuwa makaranta amma bamu san me yake faruwa da ita ba saboda ko wayarta idan muka kira bama samu.”

Ta bayyyana mana cewa sai daga baya suka samu labari cewa dalilin rashin lafiya ne yasa bata zuwa makarantar.

Sai dai a wani faifan bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta, an hangi Fatima Musa cikin yanayin rashin nutsuwa, inda jikinta yake da tabo tare da kumburi.

Yanayin da za’a iya cewa Fatima ta sha dukan kawo wuka ne daga Sa’eed wanda hakan yasa ta nemi kare kanta ta hanyar soka masa wuka.

Ku biyo mu gobe Lahadi domin jin cikakken bayani daga kowanne bangare inda wakilanmu tare da abokan karatun Fatima tare da malamansu na bangaren shari’a a jami’ar BUK, za’a ziyarci asibitin Mallam Aminu Kano domin gudanar da bincike.

Tin bayan rikicin Maryam Sanda, amaryar shekara 1 da ake zargi da caccakawa mijinta wuka, al’amarin yunkurin kisa ga mazaje daga matansu ya zama ruwan dare a arewancin Najeriya.

Daga nan anyi ta samun matsaloli tsakanin ma’aurata wanda matan suke daukar hukuncin hallaka miji.

A Kaduna an samu labarin matar data shararawa mijinta ruwan zafi.

Masu Alaka

Kotu ta bayar da belin Matar da ake zargi da caccakawa Mijinta wuka

Dabo Online

Amarya a Kano ta caccakawa mijinta wuka bayan aurensu da watanni 6

Dabo Online

‘Mijinta ne yayi mata dukan tsiya ya caka wa kanshi wukar’ – Waye me gaskiya tsakanin dangin miji da matar?

Dabo Online

Kano: Budurwa ‘yar shekara 17 ta kashe kanta saboda mahaifinta ya saki mahaifiyar ta

Dabo Online

‘Yan sandan jihar Jigawa sun cafke Matar da ta watsa wa Mijinta ruwan zafi a al’aurarshi

Dabo Online

Anyiwa Fatima Musa aure da Sa’eed a watan farko na haduwarsu bayan an rabata da wanda take so

Dabo Online
UA-131299779-2