An binne dan Najeriya da ya rasu a kasar Indiya bisa koyarwar addinin Musulunci

Tini dai aka kammala binne dalibin nan , dan Najeriya da ya rasu bayan kammala karatun Digirinshi na 2 a kasar Indiya.

DABO FM ta tabbatar da binne Sulaiman a daren ranar Alhamis 18 ga watan Yulin 2019.

Wakilin DABO FM dake kasar Indiya ya tabbatar da binne Suleiman da misalin karfe 9:17 na dare a lokacin kasar Indiya, wanda yayi dai dai da 4:48 na yamma agogon Najeriya da Nijar.

An dai binne shi ne a unguwar Amer dake garin Jaipur na jihar Rajasthan, arewacin kasar Indiya.

Sulaiman, mai shekaru 26, dan asalin jihar Adamawa, ya rasu a ranar Laraba biyo bayan matsananciyar cuta.

Hakan yana zuwa ne a dai dai lokacin da yake jiran karbar takardar shaidar kammala karatun Digirinshi na 2 a jamiā€™ar NIMS University dake kasar Indiya.

%d bloggers like this: