Home LabaraiAnyi kira ga Ministoci da su duba buktar Mutane ba ta kawunansu ba

Anyi kira ga Ministoci da su duba buktar Mutane ba ta kawunansu ba

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

An shawarci sabbin ministoci da shugaba Muhammadu Buhari ya nada
da su kasance ma su tunanin makomar al’ummar al’ummar Nijeriya ba
makomarsu bayan sun sauka mulki ba.

Alhaji Sani Bawa, Sakataren kudi na Jama’atul Nasrul Islam reshen karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, ne yayi wannan kira a lokacin da ya gana da manema labarai akan matakan da yakamata sabbin Ministocin su dauka wajen kawo matsalolin dake addabar Najeriya.

Alhaji Bawa ya kara da cewa; “Duk
bayanin da al’ummar Nijeriya ke furtawa cewar shugaban kasa Muhammadu
Buhari, ya zakulo zakakuran mutane masu masu kishin ‘yan Nijeriya da kuma
Nijeriya.”

“‘Yan Nijeriya ba za su yadda da wannan magana ba, har sai sun ga yadda sabbin ministocin suka tunkari nauyin da aka dora ma su, na shugabanci, a ma’aikatun da aka tura su.”

Daga karshe, yayi kira ga sabbin ministocin da wajibi ne su yi adalci a shugabancin da aka dora ma su, kamar yadda ya ce;

“Dadin gobe, saurin zuwa, in goben ta zo, su san abin da za su bayyana wa ‘yan Nijeriya
na abin da suka zama silar yi, na cigaban al’umma, ba na ci gaban
kansu tare da ‘ya’yansu ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00