0
Wani mamba a jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, Charles Oko Enya ya janye karar da ya shigar domin sahalewa shugaba Buhari damar sake tsaya wa takara a karo na 3.
Rahoton Dabo FM na jaridar TheCable ya rawaito cewa Mr Enya wanda shine sakataran shirye shirye na kamfe din Buhari a 2019, ya shigar da karar ne mai lambar fayal (FHC/AI/CS/90/19) a babbar kotun tarayya dake garin Abakiliki.
Yaje wa kotu da bukatar ne bisa la’akari da 137(1) (b) da 182 (1) (b) karkashin kundin tsarin mulki na shekarar 1999 wanda zai bawa shugaban kasa da gomnini damar zango na uku.
Amma daga bisani ya janye karar ne saboda jan kunne da jam’iyyar ta kasa tayi masa.
