An kashe malamin addini tare da cinnawa gawarshi Wuta a jihar Taraba.

by Dabo Online
0 comments

Wasu masu dauke da makamai sun hallaka malamin addinin Kirista a cigaba da rikicin kabilu a jihar Taraba.

Limamin da aka bayyana da Rabaren David Tanko a Kufai Adamu, dan karamar hukumar Wukari, yana kan hanyarshi ta m zuwa garin Takum domin shirin sulhu akan rikicin da kullin yake kara tsamari tsakanin kabilun Tivi da Jukun.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa; shugaban kwamitin zaman lafiya, Shiban Tikari ne ya sanar da hakan.

Ya kara da cewa; bayan sun kashe malamin, sai suka bankawa motarshi da gawarshi wuta.

Rahotannin sun bayyana cewa; ana zargin ‘yan kabilar Tibi da aikata kisan.

Bayan tuntuba don jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar da Jaridar tayi, hakanta ya gaza cimma ruwa.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00