Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Cin Nama yana kara yawaitar wari a jikin ‘Dan Adam – Masana

1 min read

Masana kiwon lafiya sun binciko cewa cin Jan Nama, ma’ana naman babbar Dabba yana kara wari a jikin Dan Adam.

Wari a jiki ‘Dan Adam yana zuwa ne a lokacin da ‘Bacteria’ take rugur-gurza sinadarin ‘Protein’ zuwa wani sinadari mai nau’in ruwa wanda ke dauke da ‘Hydrogen’.

Dabo FM ta binciko cewa Cin Jan Nama yanada matukar tasiri wajen kara yawaitar wari a jikin Dan Adam.

Bincike da aka wallafa a Mujallar Chemical Senses ta shekarar 2006 ne ya tabbatar da hakan.

Binciken ya kara da cewa; warin jiki yana matukar jin dadi idan ya samu mutum mai cin Jan Nama sosai.

Sai dai binciken yace ba iya cin naman bane yake kawo wa jikin wari, amma dai abinda yake da akwai shine, jikin masu cin Jan Nama yafi wari.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.