Labarai

Gwamnati Najeriya ta sheka ‘Al-Kazzibu’ akan ceto daliban ABU guda 3 – Dangin daliban

A jiya laraba ne dai rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bada sanarwa cewa ta ceto daliban jami’ar ABU Zaria guda 3.

Rundunar ta fitar da sanarwar ta hannun mai magana da yawunta, Yakubu Sabo, kamar yacce kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ ya rawaito.

Duk a ranar Larabar, Jami’in gwamnatin Najeriya kan harkokin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya wallafa labarin a shafinshi na Twitter.

Dabo FM ta tattaro cewa ; Bashir Ahmad ya goge rubutun, inda kuma ya roki gafara akan rubutun nashi bayan da iyalan daliban suka karyata labarin.

Wani mai amfani da shafin Twitter, Sadiq Ango, wanda yana daga cikin dangin daliban, ya bayyana cewa; “Babu sa hannun ‘yan sanda, dangin daliban guda 3 ne suka karbo yaransu bayan sun kammala biyan kudin fansa.”

Har ma ya kara da cewa; “Sai da muka shafe awanni 48 muna ciniki akan kudin fansar da muka biya aka sakar mana kanwarmu.”

Rubutun Sadiq Ango ya janyo hankalin Bashir Ahmad, lamarin da ya sa ya wallafa sabon rubutu da nufin neman afuwar mutane bisa labarin da ya wallafa “Ya zama ba dai dai ba” bayan magantuwa da ‘yan uwan daliban sukayi.

“Na cire maganar da na wallafa bayan wani daga ‘yan uwan daliban ya shaida cewa babu hannun ‘yan sanda a ceto su.”

“Nima dai farko na samu labarin ne daga kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’, bayan wasu ‘yan mintuna sai wasu gidan jaridu suka wallafa.”

“Na wallafa ne a kokari na samu lada, Ina neman afuwan akan abinda na wallafa.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin Buhari zata samar da ayyukan yi miliyan 20 a zango na biyu – Minista

Dabo Online

Buhari zai ciwo bashin dalar Amurka miliyan 890 domin yaki da sauro

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin Buhari zata samar da ayyukan yi miliyan 20 a zango na biyu – Minista

Dabo Online

Turawa sunyi amfani da maganganun PDP wajen saka Najeriya ta 1 a cin hanci -Garba Shehu

Muhammad Isma’il Makama

Babu wani ci gaba da Buhari ya samu a yaki da Boko Haram -Kungiyar Tarayyar Turai

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya amince da ginin sabuwar kwalejin ilimi a jihar Bauchi

Dabo Online
UA-131299779-2