Labarai

Nima na cancanci samun kyautar wanzar da zaman lafiya ta ‘Nobel Prize’ -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari, ta yaba da kyautar samun shaidar wanzan da zaman lafiya ta Duniya da shugaban kasar Habasha ya samu.

Shugaban kasar Habasha, Abiy Ahmad, ya karbi kyautar ne ranar Juma’a bisa dalilin hubbasarshi wajen wanzar da zaman lafiya a yankinshi.

Ayyukan sun hada da sasanta rikicin kasar Sudan tare da wanzar da zaman lafiya tsakanin kasarshi ta Habasha da kasar Eritrea.

Da yake taya shugaban kasar Habasha murna, shugaba Buhari ya bayyana kyautar a matsayin wani cigaba ga nahiyar Afirika ta fuskar samun kwanciyar hankali da nutsuwa a nahiyar.

Sai dai shugaba Buhari, ta hannun Mallam Garba Shehu, yace shugaba Buhari ma ya cancanci samun irin wannan kyautar bisa irin rawar da ya taka wajen samun nasara a kawo karshen rikicin kabilyn Jukun da Tibi.

Ya alakanta rashin samun kyautar da shugaba Buhari bai yi ba a matsayin rashin bayyanawa duniya irin kokarin da gwamatinshi take yi wajen kawo zaman lafiya a rayuwar Jama’a.

“Mu ba mu roki a ba mu kyautar Nobel ba,” in ji Garba Shehu.

Sashin Hausa na BBC yace; “Farfesa Wole Soyinka ne dan Najeriya da ya taba cin kyautar Nobel a 1986, kuma babu wanda ya sake samunta a Najeriya sabanin Afirka ta kudu da mutane da dama suka samu.

Tun bayan da aka ba wa Aby Ahmed wannan kyauta ne, shugabannin kasashe da hukumomi suke ta aike sakonnin taya shi murna musamman kan kokarin da ya yi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Eritrea a bara bayan kwashe tsawon shekaru ashirin suna takaddama.”