//
Tuesday, April 7

#JusticeForKanoKids: ‘Yan sanda sun sake kubutar da Yaran Kano 2 daga Anambra

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘Yan Sanda ta bakin kakakin ta na jihar Anambra, Haruna Muhammad, ta bada sanarwar kame wasu da ake zargin barayin yara ne a Awkan dake jihar Anambra.

Kakakin rundunar ya sanar da haka ne a ranar Asabar, 26 ga watan Oktobar 2019, inda ya tabbatar da kame wasu Mata 3 dauke da Yara 2 Maza, ‘yan kimanin shekaru 2 da 4.

Sati 2 da suka gabata ne Kwamishinan ‘Yan Sanda na kano ya damke wasu da ake zargin sun sace yara a Kano, su canza musu addini su kuma siyar dasu a Anambra, inda hukumar ta tseratar da yara 9.

A rahoton da Premium Times ta fitar ta shaida cewa yan sandan jihar Anambra sun samu nasarar kubutar da yaran guda 2 ne a wani sumame da suka kai ranar Talata, bayan rahotanni da suka samu tare da bincike daga bangaren kwararrun hukumar.

Masu Alaƙa  Rigar 'Yanci: Dama nasan za'a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin 'yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

A ta bakin rundunar tace an kame wanda ake zargin a kasuwar Nkpor, shatale-talen Tarzan a cikin karamar hukumar Idemili ta Arewa dake Anambra.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020