Labarai

An shafe kwanaki 150 da karin Albashin N30,000 a takarda

A ranar Alhamis, 18 gawatan Afrilun 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu na aminta da karin biyan albashin ma’aikatan Najeriya daga N18,000 zuwa N30,000.

Har kawo yanzu dai karar kararrawar wayar ma’aikatan bata chanza salo ba, domin kuwa har zuwa yanzu babu batun biyan su kudin.

A cigaba da wasan ‘yar ganin laifi da akance gwamnatin shugaba Buhari ta kware a kai, gwamnatin dai ta bayyana cewa kungiyar kwadago ce ta hana a fara biyan albashin bisa wasu tsare-tsare na gwamnatin da kungiyar taki amincewa dashi.

DABO FM ta tattara cewa; zuwa yanzu dai , an shafe kwanaki kwanaki 150 daga ranar da shugaba Buhari ya sanya hannu da dokar.

Abin lura shine; Fadar gwamnatin tarayya ta bayyana dokar a matsayin wacce zata fara aiki nan take, sai dai har yanzu dokar bata kai ga taka kowa ba.

Hakan yana da nasaba da rashin daidaito da aka samu daga bangaren gwamnatin da kungiyar Kwadago.

Ana dai san ran sake zama domin saho kan matsalar a karshen watan Satumba.

Gwamnatin ta sanar da karin harajin kayayyaki a kasar daga kasho biyar zuwa kaso 7.5 a kokarinta da tace tana tarin kudaden da zata iya biyan albashin ne.

Masu Alaka

Kungiyar Kwadago ta bawa gwamnan jihar Niger wa’adin kwana 21 akan biyan albashin N30,000

Dabo Online

Murna ta cika masu bautar Kasa bayan jin kararrawar alawus na N33,000

Dabo Online

Tambuwal na Sokoto ya bayar da umarnin fara biyan sabon albashi

Dabo Online

Karin Albashi: Majalissar Dattijai ta amince da karin albashin N30,000

Dangalan Muhammad Aliyu

Sabon jadawalin Albashin jami’an ‘Yan Sanda

Dabo Online

Sai mun rage ma’aikata zamu iya biyan mafi karancin albashi – Ministan Kwadago

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2