An tilasta min yin magudi a Zaben 2019 – Baturen Zabe

Baturen babban zaben 2019 na hukumar INEC a jihar Kwara, Garba Madami yace wasu yan siyasa sun so siyanshi da kudi domin ya murde zaben 2019 a jihar Kwara.


Madami ya bayyana haka ne a yau Litinin a wajen daurin auren ‘yar shi a garin Minna dake jihar Niger a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa baturen zaben, Mr Garba Madami ya bayyana cewa;

“Na samu matsin lamba da yunkurin tilastawa daga ‘yan siyasa wandanda suka ce zasu bani kudi domin nayi magudi a zaben 2019 amma naki karba da kuma kin amincewa da yin magudin.”


“Yanayin aikinmu a hukumar zabe ta INEC, yana da matukar wahala hadi da barazana.”

“Ya rage na mutum, tsakaninshi da Allah, yayi riko da gaskiya da amana ko kuma yayi cuta ya ci amana. Kuma mutum zai iya karewa a gidan yari.”

Mr Garba, ya koka kan yacce ‘yan siyas ke amfani da kudi akan harkar zabe da ‘yan siyasar da suke ganin zasu iya siyan mutane domin aikata mummunar ta’asar da suke so.

“Tabbas ‘yan siyasa suna da kudi kuma wasu daga cikinsu suna jin cewa zasu iya siyan kowa da kudi.”


“Magana ake ta rikon amana; ya rage na naka tayi taka tsan-tsan wajen rike wannan amanar.”

“Abinda nayi a jihar Kwara tun kafin a fara zabe, na fadawa duniya cewa babu wani adadin kudi da za’a iya siya ta dasu.


“Na tabbatar musu da cewa bazanyi magudi ba, abinda mutane suka zaba, shi za’a gani.

Baturen zaben yayi tsokaci kan batun kararraki 765 da aka kai gaban kotunan sauraron karar zabe, inda ya lamarin da karancin dimokradiyyamai kyau tsakanin jami’iyyun siyasar Najeriya.

%d bloggers like this: