Adamawa: Fintiri ya kwace filayen makaratu da aka rabawa wasu shafaffu da mai

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya kwace dukkanin filayen makarantu da aka rawaba wasu mutane a jihar.

Darkatan watsa labarai da hulda da mutane na gwamnan jihar, Solomon Kumangar ne ya bayyanawa manema labarai haka a ranar Juma’a a garin Yola.

Kumangar ya bayyana cewa mutanen da aka baiwa filayen makarantun firamare da sakandire sun fara ginewa a fadin jihar musamman a kananan hukumomin Yola, Mubi da Michika.

Kumangar ya kara da cewa, gwamnatin Gwamnan Fintiri da take da muradin farfado da harkar ilimin jihar ta bada umarnin biyan naira biliyan 8.2 ga hukumar kula da ilimi tin daga tushe ‘UBEC’ domin inganta harkokin ilimin.

“A cikin shirin farfado da ilimin, gwamnati ta mayar da ilimi kyauta tare da tilastawa dukkanin wadanda basa zuwa makaranta samun ilimin.”

“Gwmnatin tayi shirin gyaran makarantu 5000 a cikin wata 6 masu zuwa.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog