Buhari ya yi kiran ‘yan Najeriya su yi koyi da kyawawan dabi’un Yesu

Shugaban ya ce Najeriya tana bukatar yan kasar su yi koyi da dabi'un Yesu.

Karatun minti 1
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon murnar bikin Kirsimeti ga al’ummar Najeriya musamman mabiya addinin Kiristanci.

Buhari ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafukansa na sada zumunta da safiyar yau Juma’a.

“Ina mika sakon taya murna ga yan uwana Kiristoci maza da mata da dukkannin yan Najeriya a wannan lokacin farin ciki na bikin Kirsimetin shekarar 2020 na murna da haihuwar Yesu.

Shugaban ya yi kira ga al’ummar Najeriya wajen yin amfani da wannan lokaci da kuma koyarwar addinin domin tabbatar da soyayyar juna, jinkai da zaman lafiya.

Shugaban ya kuma yi kira ga al’umma da su yi koyi da kyawawan dabi’un Yesu, wadanda ya ce a yanzu Najeriya irin halayen ta ke bukata daga yan kasar musamman a wannan lokacin da yace kasar tana fama da matsalolin ta’addanci, matsin tattalin arziki, garkuwa da mutane da cutar Kwabid-19.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog