Labarai

Ana dambarwa kan motocin yakin da aka shigo da su Najeriya

Sashin Hausa na Rediyo Faransa ya rawaito cewa;

Kawo yanzu mahukuntan kasashen Najeriya, Kamaru daNijar ba su fayyace ainihin mamallakin motocin yakin masu
silke da aka shigo da su Najeriya ba.

Ana ci gaba da samun dambarwar ne dangane da hakikanin mamallakin motocin yaki masu silke guda shida da Jami ‘an
tsaron Najeriya suka kama a kan iyakar kasar da Kamaru da ke garin Konkol na karamar Hukummar Maiha ta jihar Adamawa.


Majiyoyi sun ce, an yi nufin isar da motocin yakin ne ga hukumomin Jamhuriyar Nijar, amma kawo yanzu mahukuntan kasashen Najeriya da Kamaru ba su fayyace ainihin mamallakin motocin ba.

A yayinda bayanai ke cewa, gwamnatin Nijar ce mamallakiyar motocin yakin, wasu rahotanni cewa suka yi, na Kamaru ne,
yayinda wasu majiyoyin suka danganta motocin da kasar Amurka.

Tuni Kwamandan bataliyar sojoji ta 23, S.G. Mohammed ya mika motocin yakin ga Hukumar Hana Fasa Kauri wato
Kwastam, reshen jihar Adamawa da

Hukumar Kwastam ta shirya gudanar da taron manema labarai kan wannan dambarwa a birin Yola, amma daga bisani aka soke taron saboda an mika batun ga hukumomin birnin tarayya Abuja.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, a halin yanzu, shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kanar Hameed Ali mai ritaya, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan al’amarin.


Majiyar Kwastam ta ce, an kama motocin ne saboda rashin takardun izinin safarar su zuwa wata kasa, yayinda wasu bayanan ke cewa, gwamnatin Amurka ce ta yi wa sojojin kasar Nijar kyautar motocin.

Karin Labarai

Masu Alaka

Shugaban INEC yayi murabus?

Dabo Online

‘Fasa Kwauri’ ya karu duk da rufe iyakokin Najeriya

Dabo Online

Matashin daya sha ruwan Kwata saboda murnar cin zaben Buhari ya rasu

Dangalan Muhammad Aliyu

Gwamnatin tarayya zata rage harajin “Giya”

Dabo Online

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Zaben2019: Hukumar INEC ta dage zabe, zuwa 23 ga wata

Dabo Online
UA-131299779-2