Bincike

Kashi 30 cikin 100 na yara a yankin Arewa maso Yamma basa zuwa makaranta – UNICEF

UNICEF ta bayyana cewa akwai kimanin sama da kaso 30 cikin dari na kananan yara da basa zuwa makarantar Boko a yankin Arewa maso Yamma.

Hukumar ta bayyana haka ne ta hannun jami’inta, Mukhtar Muntaka a wani taron tattauana matsallolin yara da hukumar ta shirya a jihar Kano.

Mukhtar, ya bayyana cewa babu jihar Kaduna a lissafin.

Ya ce jihohin dake yankin sun hada da
Kano, Katsina, Sokoto, Zamfara da Kebbi
amma sai dai wannan matsala bai shafi
jihar Kaduna ba.

“Ilimin firamare kyauta ne kuma dole ne ga
yara kanana saidai bisa ga sakamakon
bincike da aka gudanar ya nuna cewa yara
akalla miliyan 10.5 masu shekaru 5 zuwa 14
basa makarantar boko a Najeriya.

“Sakamakon binciken da muka gudanar ya
nuna cewa yara kashi 61 bisa 100 masu
shekaru 6 zuwa 11 da yara kashi 35.6 bisa
100 ‘yan watanni 36 zuwa 59 ne ke zuwa
makarantar boko a Najeriya.

Karin Labarai

UA-131299779-2