Labarai

Mabiyin Kwankwasiyya ne ya hada labaran ranar daurin auren Buhari da Sadiya Umar – DSS

A ranar Juma’a, mai kakarin hukumar DSS, Peter Afunanya, ta tabbatar da kamun wani Sulaiman Kabiru, wanda ake ya fara hada labaran auren shugaba Buhari da Minista Sadiya Umar Faruk.

Bayan an bayyanashi a babban ofishin hukumar, Mista Peter Afunanya ya ce, Sulaiman ya amsa laifin da ake zarginshi da aikatawa.

Haka zalika hukumar ta tabbatar da cewa Sulaiman, mabiyi ne ga darikar Kwankwasiyya ta tsohon gwamnan Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso.

“A shekarar 2019, tsakanin watan Agusta da Oktoba, wata bidiyon sharri ta bayyana a fadin Najeriya da ke nuna cewa shugaban kasa na shirin aure da daya daga cikin ministocinsa.”

“Ta farko itace ministar Ilimi, Hajiya Zainab Ahmad sannan kuma ministar walwala da jin dadin al’umma, Hajiya Sadiya Farouq.”

Sunansa Kabiru Mohammed. Dan asalin jihar Kano ne, Yana da shekaru 32. Yayi karatun difloma a ilmin Hausa da Fulfulde a kwalejin ilimin tarayya ta Kano.”

“Ya tona asirin kansa kuma bincike ya nuna dukkan yadda suka hada bidiyoyin da yadawa.” – cewar Mista Peter, Fassarar sashin Hausa na Legit.ng

DABO FM ta tattara cewa, faifan bidiyon da aka rika yadawa a wancen lokacin ya kunshi ranar da aka sa domin daurin auren, tare da sanya lokacin da wurin daurin auren.

Karin Labarai

UA-131299779-2