Home LabaraiUwargida ta caccakawa Mijinta wuka a jihar Kaduna

Uwargida ta caccakawa Mijinta wuka a jihar Kaduna

by Dabo Online
0 comments

An zargi wata mata a jihar Kaduna da caccakawa Mijinta wuka a jihar dake arewa maso yammacin Najeriya.

Matar da ake zargi mai suna Aisha, ta caccakawa mijin nata Yahaya A Maiyaki wukar da safiyar Juma’ar 25 ga watan Yulin 2019.

DABO FM ta tattaro cewa; Aisha ta cakawa mijin nata wuka a ciki har sau biyu, lamarin da ya janyo tayi masa mummunan rauni. Har yanzu dai ba’asan musabbabin al’amarin ba.

Yanzu haka dai yana asibiti domin karbar kulawa, ita kuwa matar da ake zargi da aikata mummunan laifi ta tsare.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana cewa tini ta tsuduma cikin bincike.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00