//
Thursday, April 2

Babu shirin bude iyakoki ‘boda’ a halin yanzu – Buhari

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ba yanzu gwamnatinshi zata bude iyakokin kasar da ta rufe ba.

Shugaban yace baza a bude iyakokin ba har sai kwamitin da aka kafa kan lamarin ya kammala bincike. Shugaban yace bayan kammala binciken, sai gwamnati ta gamsu da abinda binciken ya tattara.

DABO FM ta tattara cewar shugaban ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da yayi shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo a taron zuba hannun jarin kasashen Afirika da Burtaniyata wanda akeyi a can birnin Landan na kasar ta Burtaniya.

Shugaban yace Najeriya bata rufe iyakokinta domin hana shigowa da Shinkafa dunguringum cikin kasar ba, sai dai bisa dalilin yacce ake yin fasa kaurin makamai da miyagun kwayoyi.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamnoni: Ku zabi gwamnonin da jam'iyyar APC ta tsayar takara kawai - Buhari

Yace bazai runtsa ido yaga matasan Najeriya suna lalacewa ta hanyar samun kwayoyi da ake fasa kaurinsu da kuma kananan makamai dake kawo wa sha’anin tsaron Najeriya cikas.

“A duk lokacin da aka tsare motocin da suke shigo da kayan abinci, ana ganin lullubin biri domin ana samun miyagun kwayoyi da kananun makamai a kasan abincin da suka dauko. Wannan yana da matukar illa ga kowacce kasa.”

Ya bayyana damuwarshi bisa ga yadda rufe iyakokin kasar ya kawo wa kasashen dake makwabtaka da Najeriya koma baya, sai dai yace “baza mu bar kasarmu musamman matasanmu” su lalace ba.

Da yake nuna fahimtarshi ga matakin Najeriya, shugaban kasar ta Ghana, Nana Akufo-Adda, ya roki gwamnatin Najeriya da ta sauya salon kare yan kasarta ta domin mutanen kasar Ghana da yawansu na harkokin kasuwancinsu da kasuwannin Najeriya.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020