Home LabaraiDa makin ‘F9’ a darrusan Lissafi da Turanci jami’ar ABU ta bawa CJN Tanko gurbin karatu

Da makin ‘F9’ a darrusan Lissafi da Turanci jami’ar ABU ta bawa CJN Tanko gurbin karatu

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Rahotanni sun tabbatar da jami’ar Ahmadu Bello ta bawa Alkalin alkalai, CJN Tanko Muhammed gurbin karatu ba tare da ya samu makin da ake bukata ba a darasin Lissafi da Turanci.

Rahoton Dabo FM ya bayyana wannan yazo ne cikin takardun sakamakon CJN Tanko wanda ya nuna yana da makin ‘Credit’ 3 da ‘Pass’ 2, kamar yadda jaridar DailyTimeTV ta fitar.

Kamar yadda sakamakon jarabawar sa ta yammacin Afirka, WAEC ta nuna, wadda Jastis Tanko ya zauna a 1973, Jastis ya samu makin ‘C5’ a Darasin Hausa, kana ‘C4’ a Darasin Tarihi da ‘C6’ a Darasin Ilimin Addini (IRK).

Haka kuma ya samu makin ‘Pass’ a ilimin kimiyya wato Kemistire da Darasin koyon harshen Larabci. Duba hotuna a kasa..

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00