Manyan Najeriya basa kauna ta – Shugaba Buhari

Daga shashin Hausa na BBC “

“Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce bai damu da rashin kaunar da manyan kasar suke nuna masa ba.

A wata hira ta musamman da gidan talabijin din kasar (NTA), Shugaba Buhari ya ce shi yana da yakinin cewa babu wani a kasar da zai iya samun kuri’un da ya samu a zabensa na farko da na biyu.

Ya ce yana da masaniyar cewa manyan kasar kwata-kwata ba sa kaunarsa, inda ya ce hakan ba ya damun sa ko kadan.

Da aka tambayi shi kan kamun ludayinsa dangane da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa a sabuwar gwamnatinsa da za ta fara ranar 29 ga wannan watan, sai Buhari ya ce “Zan kara wa ‘yan sanda da kotu karfi” yadda ba za su tausaya wa masu laifi ba.”

Masu Alaƙa  Zuwa ga Shugaba Buhari: Idan kai mai gaskiya ne, ka tonawa barayin kusa da kai asiri - Gwamnan Akwa Ibom

Buhari ya sha alwashin cewa duk masu yi masa kallon yana ‘tafiyar hawainiya’ to za su kunyata domin za a ga wani Buhari ne daban.

Shugaba Buhari ya kuma dora alhakin lalacewar jami’an tsaro musamman sojoji ga shugabannin da suka yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2015, inda ya ce a lokacin ne aka samu tabarbarewar aikin da kuma rashawa da cin hanci.

Sai dai Buhari ya yaba wa masu rike da mukaman jagorancin sha’anin tsaro, inda har ya nuna cewa gwamnatinsa ta yi nasarar karya kungiyar Boko Haram.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

Masu Alaƙa  Bama samun Wutar Lantarki sai kazo Daura - Masarautar Daura ta fadawa Buhari
%d bloggers like this: