An gudanar da tiyatar kwakwalwa ta farko a tarihin jihar Kano a sabon asibitin Muhammad Buhari specialist Hospital dake Giginyu.

Tiyatar da aka gudanar a cikin makonnan biyo bayan tagomashin kayan aiki tiyatar da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta samar a shirinta na inganta fannin lafiya a jihar kamar yadda baban mataimakin gwamnan akan harkar kafofin sada zumunta ya wallafa a shafinshi na instagram a ranar asabar.
Tiyatar ita ce ta farko a tarihin jihar dama yankin arewa maso yammaci da gabashin kasar Najeriya.
Asibitin da gwamnatin jihar ta bude a watan Disambar shekarar 2017.

Yayin gudanar da aikin. cc: AA Ibrahim
Gwamnatin jihar karkashin jagoranci Dr Abdullahi Umar Ganduje itace ta jagoranci bude wannan asibitin da aka kashe kimanin naira biliyan hudu da dugo biyu (₦4.2b) tin bayan da gwamnatocin jihar suka watsar da ginin asibitin shekaru goma da suka wuce.
