Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Azumin Ramadana: Kayan abinci sunyi tashin “Tashin Hankali”

2 min read

Gabanin karatowar watan azumin Ramadan da musulman duniya suke azumta, kayayyakin amfanin yau da kullin a fadin Najeriya sunyi tashin gwauron zabi.

Kamfain dillancin labarai na NAjeriya, NAN, ya rawaito cewa a jihar Legas, kayayyakin masarufi da kayan gwarin sunfi tashi sosai inda aka bayyana su da yin tsada sosai.

Wakilin jihar Legas ya garzaya wasu kasuwanni a jihar Legas inda ya gano cewa kayan abinci musamman kayan gwari sunyi tashin gwauron zabi duk a saboda tunkarowar azumi.

Kwandan tumatir yayi tashi gwauron zabi, inda a makon daya wuce ake siyar dashi N5000 inda a yanzu kuma ya koma N12,000.

Suma Attaruhu da albasa sunyi tashin kamar babu gobe.

Mutane da dama sun fara kokawa kan yadda ‘yan kasuwa suka maida watan Ramadan lokacin tsawwala wa mutani tsada.

Wani dankasuwa ya cewa “Akwai yiwuwar samun sauki idan aka fara shigo da kayan miya zuwa kasuwannin jihar har daga kasar Kamaru.”

Daga bangaren binciken da muka gudanar a nan Dabo FM, mun tattauna da wasu mutane a jihar Kano, inda suma suka bayyana cewa tashin kayan gwarin yazo har jihar Kano, inda suma suka bayyana rashin jin dadinsu akan lamarin

A kwanakin nan malaman addinin musulunci sunyi ta kira ga yan kasuwa dasu rika sauko da farashin kayyayakinsu a lokacin azumi domin samun rabauta a cikin watan da yake mai alfarma.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.