Copyrighted.com Registered & Protected

Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 169.74 don gyaran tituna 10

Babban Majalissar Zartarwa ta tarayya, FEC, ta amince da kashe Naira biliyan 169.74 domin gina sababbin da kaskwarimar wasu tituna a fadin tarayyar Najeriya.

Babban mai baiwa Ministan ayyuka na kasa shawara, Hakeem Bello ne ya fitarwa da manema labarai sanarwar a yau Asabar, 04/05/2019.

Yace ayyukan zasu taimaka wajen inganta harkar sufuri domin dawo da martabar titunan tarayyar kasar a shirin da gwamnati takeyi na inganta titunan.

Bello ya kara da cewa, amincewar kudin yana zuwa ne bayan da Ministan ayyuka, Mr Babatunde Fashola ya mika bukatun ayyukan titunan.

Yace titunan da za’a gyara sun hada da Titin Umuahia-Ikot Ekpene, Titin Calabar-Oban-Ekang, Titin Ado-Ekiti-Igede-Aramoko-Itawure, Funtua-Dandume-Titin Iyakar Kaduna da Titin Makurdi-Gboko-Katsina-Ala.

Masu Alaƙa  Sai na kashe Buhari - Victor Odungide

Sauran sun hada da; tsohon titin Enugu-Onitsha, Karin hannu daya a titin Aba-Ikot Ekpene mai tsawon kilomita 74, Titin Billiri-Filiya- Iyakar jihar Taraba. Ginin sabon titin Yola-Fufure-Guri, Titi da titi mai tsawon kilomita 4 a karamar Gaya dake jihar Kano.

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: