‘Azumin Sittu Shawwal bashida asali, yin shi Bidi’a ne’

Sheikh Dr Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa yin azumin sittu Shawwal bashida asali, asalima yinshi Bidi’a ne bisa wani babi daya karanto daga Cikin Muwadda Maliku.

Sheikh Gumi yayi karatunne a 20 ga watan Oktobar 2018, sai dai ya wallafa karatunne dai dai lokacin da al’ummar musulmi suke daukar niyyar fara azumtar kwanaki 6 na watan Shawwal kamar yadda binciken DaboFM ta tabbatar.

Daga cikin littafin Muwadda wanda Sheikh Gumi ya karanta,yace; “Yin azumi 6 bayan an bude baki,na Ramadan. Ban taba gani daga magabata ba, baizo min cewa wai yana azumin bayan Ramadan ba, kuma suna tsoron ma zai iya zama Bidi’a.”

Binciken DaboFM ya gano inda Shiekh Gumi yake cewa hadisan da ake malamai suke kafa hujja dashi na azumin Shawwal ba ingantacce bane.

Wannan Hadisin da ake rawaito wa “Wanda ya raka azumin Ramadan da azumtar kwanaki 6 na Shawwal…’ Bidi’a ne.”

%d bloggers like this: