Ba a ga jinjirin watan Muharram a Najeriya ba – Kwamitin ganin wata

Karatun minti 1

Kwamitin ganin wata na Sarkin Musulmin Najeriya ya ce bai samu sahihin rahotan ganin jinjirin watan Muharram a fadin Najeriya ba.

Kwamitin ya ce ranar Alhamis da ta yi dai dai da 20 ga watan Agusta 2020, ita ce 30 ga watan Dhul Hajji a Najeriya.

DABO FM ta tattara cewa kwamitin ya tabbatar da cewa an samu rahotannin ganin watan a wasu jihohin Najeriya, sai dai a cewarsu ba sahihai bane, ba su da inganci.

Kwamitin ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Twitter.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog