Ba’a ga Sarkin Kano Sunusi ko wakilinshi a taron rantsar da Ganduje ba

Daga rahotanni da muke samu daga wasu wakilanmu tare da mahalarta taron ranar rantsuar gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje sunce, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II bai halarci taron ba.

Ana dai bikin rantsar da Ganduje yau Laraba, 29 ga watan Mayun 2019 a babban filin wasa na Sani Abacha dake kwaryar birnin Kano.

Sai dai rahotannin sunce Mai Martaba Sarki Bichi, ALhaji Aminu Ado Bayero tare da wasu daga cikin takwarorinshi wadanda gwamnatin Ganduje ta kirkira sun samu halartar taron.

Sarkin Rano ya samu halarta, inda a yanzu da muke hada wannan rahotan, Sarkin Gaya da Karayae, rahotanni sun bayyana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa wajen taron.

%d bloggers like this: