Ba’a kama ‘Yan Arewa 123 da aka tsare a jihar Legas da miyagun makamai ba -‘Yan Sanda

by Dabo Online
0 comments

A jiya Juma’a 29 ga watan Agusta, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tsare wasu mutane guda 123 wadanda suka shiga jihar daga jihohin Arewa.

Rundunar ‘Yan sanda ta bayyana cewa ta samu labarin shigowar mutanen daga wani rahoto da aike mata cewa; “Kimanin mutane 300 sun shigo jihar a cikin wata babbar Mota dauke da babura.”

DABO FM ta binciko cewa; Rundanar tace ta iske Mutane 123, da Babura 48 a cikin motar.

Sai dai ta bayyana cewa bayan binciken data gudanar, bata samu ko da mutum daya a cikinsu da makami ba, hasalima sun shaida mata cewa sunzo jihar ne domin neman Kudi.

05BF85F6 F93C 43AD B08B 4A73968E77F0 - Dabo FM

“Yawansu ‘yan jihar Jigawa ne, kuma 48 daga cikinsu sun ce Babura dake cikin motar nasu ne.”

“Banda Babura, ba’a samu komai a tare dasu ba.”

22C845DC D957 4528 BD41 91CB7E94A464 - Dabo FM

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00