Kaduna: Masu garkuwa da Mutane sun sace wanda yaje biyan kudin fansa

Yan bindigar dai sun sace, Yusuf Ishak a dai dai lokacin da ya kai musu kudin fansar abokin aikinshi da aka sace a unguwar Rigasa ta jihar Kaduna.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito yacce mutumin ya bada labarin abinda ya faru tsakaninshi da ‘yan Bindigar.

Ishak yace; “An sake ni ne da kimanin karfe 12:00 na ranar Litinin tare da Abdulrashid Lawal. Bayan da na kai wa masu garkuwa da mutane kudin fansar inda su ka amince za su karbi N350,000.”

Wannan Malamin asibiti da ke aiki a Sardauna Memorial Medical Foundation da ke Kaduna ya ce kafin a sake su, sai da su ka kara biyan N300, 000 a kan kudin da su ka bada. Ishak ya ce sun wahala ainun.

Ya kara da cewa: “Gaskiya ban taba tunanin zan fito da rai ba, bayan irin azabar da a ka guma mani a hannun wadannan mutane. Da idanun mu duk a rufe, haka mu ke cin abinci. Yanzu ma mu na asibiti.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.