Labarai

Dukkanin wakilan jami’iyyu sun aminta da’a soke zabe na 2 da akayi a mazabar Gama – Umar Yakasai

Dukkanin wakilan jami’iyyun da suka fafata a zaben gwamnan jihar Kano sun aminta da’a soke zaben da aka sake yi ran 9 ga watan Mayu a mazabar Gama dake karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

DABO FM ta binciko cewa; Jami’in akwati na jami’iyyar PDP, Umat Tanko Yakasai ne ya bayyana haka ne yayin da bada shaida a gaban kotun da PDP take kalubalantar nasar Dr Ganduje.

Ya bayyanawa kotu cewa dukkanin wakilan jami’iyya sun amince a rubuce domin soke sakamakon guk wata rumfar zabe da aka samu tarzoma.

Da yake fadin yacce zaben mazabar Gama a zagaye na biyu ya kasance, Yakasai, yace an bayyana zaben Gama zaben da aka rika samun kuri’ar da ta fi yawan adadin mutanen da aka tantance.

Ya kuma kara da cewa m; hatsaniya ta barke a daidai lokacin da ake tattaro sakamako a cibiyar tattara sakamakon zabe ta karamar hukuma, lamarin da yasa wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba suka kone takardar tattaro sakamakon zabe da INEC ta bayar.

Ya bayyana cewa hakan ce ta sakashi tserewa zuwa wani dan daki da yayi mafaka ya kuma rufe kanshi tare da sauran wasu kayan ayyukan zabe.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kotun ‘Allah-ya-isa’ ta fatattaki Akitu tun ba’a je ko ina ba

Muhammad Isma’il Makama

Kano: Kotun daukaka kara ta tabbatar wa Hon Shamsuddeen Dambazau na APC kujerarsa

Muhammad Isma’il Makama

Alkalin alkalai ya sake dakatar da shari’ar Abba da Ganduje

Dabo Online

‘Yan Kwankwasiyya sun dauki hanyar kawo wa Shari’ar ‘Abba Gida-Gida’ cikas

Dabo Online

Kotu ta kori karar Dan Majalissar PDP ta tabbatar da APC

Dabo Online

Kotu tayi watsi da karar Atiku, Buhari yayi nasara a kotun zabe

Dabo Online
UA-131299779-2