Bincike Kiwon Lafiya

Jerin kasashen da Korobairas ba ta shiga ba

Cutar Koronabairas, anooba ce da ta karade duniya baki daya wadda a yau babu kasa shahararriya a fadin duniya ta cutar ba ta bulla ba.

Sai dai bincike ya nuna akwai kasashe da kuma tsiburan da har zuwa yau cutar ma’aikayar lafiya ta kasar ba ta tabbatar da samun wanda ya kamu da cutar ba.

Bisa binciken masana, DABO FM ta tattara cewar zuwa yanzu cutar Koronabairas ta kama sama da mutane miliyan 2.79 tare da mutuwar sama da mutane 196,000, kamar yadda kiduddugar jami’ar John Hopkins ta kasar Amurka ta nuna.

Fara wa nahiyar Afirika, kiduddugar ta tabbatar da rashin samun cutar a kasashe 2 kacal daga cikin kasashe 54 da suke nahiyar Afrika.

Kasashen sun hada da Lesotho dake makwabtakar kusa da kasar Afirika ta Kudu da kuma Tsibirin Comoros dake kusa da kasar Mozambique.

A sauran nahiyoyi akwai kasar Kiribati, Tsibirin Marshall, Tarayyar Micronesia, kasar Nauru, Palau, Samoa, Tsibirin Solomon, kasar Tajikistan, Tonga, Turkmenistan, Tuvalu, Vanuatu da kasar Koriya ta Arewa.

Duk da wasu masu fashin baki su na ganin ‘kasar Koriya ta Arewa ta boye wa duniya batun da take ciki akan Korobairas. Sai dai ma’aikatar lafiyar kasar ba ta tabbatar da bullar cutar ba.

Zuwa yanzu dai a ranar 25 ga watan Afrilun 2020, mutane kusan 29,000 ne suka kamu da cutar a nahiyar Afrika in da a kasar Amurka cutar ta hallaka sama da mutane 52,000.

Karin Labarai

UA-131299779-2