Bama samun Wutar Lantarki sai kazo Daura – Masarautar Daura ta fadawa Buhari

Masu sarautar gargajiya na kananan hukumomi 5 da suka hada garin Daura, sun fadawa shugaba Muhammadu Buhari cewa; suna samun wutar lantarki tsayayyar wutar idan yazo garin.

Sun bayyana haka ne a yayin ziyarsu ga shugaban kasa domin taya murnar bikin babbar Sallah.

Daily Trust ta rawaito cewa; daga cikin shuwagabannin, Muhammad Saleh yace; “Duk lokacin da shugaban kasa yazo Daura, muna morar wutar Lantarki ta awanni 24 a kullin. Amma da zarar bayanan, shikenan wutar ta zama babu tabbas.”

Ya kuma yaba wa shugaban bisa sanya hannun akan gina sabuwar Makarantar ‘Polytechnic’ a garin na Daura jim kadan bayan da sukayi korafi kan cewa suna bukatar makarantar gaba da Sakandire.

Ya kuma kara da yin nuni da cewa sakamakon rashin aikin yi, satar mota da sauran laifuka suna karuwa a garin.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.