Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Jami’an Najeriya suna hana Likitoci a Indiya baiwa Zakzaky kulawar da ta dace

2 min read

‘Yan Shi’ar kasar Indiya sun koka kan yacce jami’an Najeriya suke hana ruwa gudu yayin da Likitoci suke duba lafiyar shugaban IMN, Sheikh Al Zakzaky.

DABO FM ta tabbatar da hakan bayan zantawa da wasu daga cikin mabiya Shi’a a kasar Indiya.

Yanzu haka kungiyoyin Shi’a da dama na Kasar ta Indiya suna shirya taron gangami da Zanga-zanga bisa nuna rashin jin dadinsu na yacce jami’an tsaron Najeriya suke kawo Likitocin dake kula da Sheikh Zakzaky cikas.

Shugaban kungiyar Hindi Resistance, Moula Imam Hussain ya bayyana cewa; “Sheikh Zakzaky bai tsira a Indiya ba ma.”

“Mutanen da suka zo tare da shi daga Najeriya, tin a filin jiragen suka haduwa da wasu gamayyar mutanen, suka kore mu.”

“A yanzu ma, sun hana wasu likitocin da a baya sukaje Najeriya domin dubashi, sun hanasu su ganshi.”

“Ban taba ganin yawan masu tsaro irin haka ba, yanzu haka ma zargi muke so suke su hallaka shi.”

Daga karshe ya bayyana mana cewa bazasu kyale haka ta faru ba domin a cewarshi; “Za’a ga ko suwaye ‘yan shi’ar Indiya, don bazamu bari haka ta faru ba.”

“Yau ce babbar ranar jarrabawar ‘yan Shia a Indiya, zamu fito mu kare Sheikh Zakzaky.”

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.