Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Akwai alamun Sheikh Zakzaky zai koma Najeriya cikin kwanaki 3

2 min read

Shugaban kungiyar IMN a Naajeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, wanda a yanzu haka yake kasar Indiya ya bayyana cewa zai dawo kasa Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da yace babu amfani zuwanshi kasar saboda jami’an Najeriya suna hana a basu taimakon da suke bukata.

DABO FM ta samu rahoto daga chan kasar ta Indiya, kasancewar wasu wakilanmu suna birnin Gurugaram na jihar Hariyana a yanzu haka; cewa Al-Zakzaky ya fara shirin dawowa Najeriya.

A cikin wani sakon murya da wakilanmu suka aiko mana bayan zantawa da wasu yan kungiyar Shia dake asibitin Medanta, ya tabbatar da rashin jin dadin zaman asibitin da Al-Zakzaky da matarshi suke yi.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa; An turo wasu sabbin Likitoci wadanda basu yadda dasu ba domin su duba lafiyar Sheikh Zakzaky tare da matarshi, lamarin da suka ki amincewa da dashi bisa hujjojar cewa “Basu yadda da Likitocin ba.”

Majiyoyin kusa da Malamin sunce; “Zasu dawo Najeriya domin sake shirin tafiya wata kasar, tinda kotu ta amince zasu iya tafiya kasar waje neman magani.”

Sun bayyana mana cewa; kasashen Malaysia da Indunusia sun nemi Sheikh Zakzaky ya je kasar domin su kula da lafiyarshi da iyalin nashi.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da yanayin jami’an da suke zaune tare da Zakzaky a yayin zamanshi a cikin Asibitin Medanta dake jihar Hariyana, yanayin tsaro ne tamkar a gidan yari.

Sun bayyana cewa ana hana shi katabus da sukuni wanda hakan yasa dukkanin wadanda suke tare dashi suke kokawa, inda har aka jiyo shi Sheikh Zakzaky yana cewa; “Zamanshi a Najeriya ma ba’a tsareshi kamar haka.”

Rahotannin sunce gwamnatin kasar Indiya tana shirin tisa keyar Al-Zakzaky zuwa Najeriya, biyo bayan barazanar zaman lafiyar kasarta da mabiya Shi’a yunkurin shiga zanga-zanga domin neman a sararwa Zakzaky.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.