Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce sake gina yankin arewa maso gabashin Najeriya shine babban kudirin gwamnatin su.
“Damuwar sake gina yankin arewa maso gabasi, shine babban kalubalen da muka saka a gaba a matsayinmu na gwamnati.”
Osibanjo ya bayyana haka ne dai dai lokacin da yakai ziyarar bude ayyukan da gwamnatin jihar Borno, karkashin gwamna Kasshim Shattima tayi.
“Ya kasance shine abinda wannan gwamnatin ta saka a gaba.” Osinbajo ya bada tabbacin cigaba da shirin da gwamnatin takeyi na ganin anyi doka akan hukumar farfado da yankin Arewa maso Gabas, yankin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kassara.
Ya kuma godewa gwamnan bisa saka sunanshi da akayi a daya daga cikin makarantu 40 da jagoranci budewar.
Daga karshe ya yabawa gwamnan jihar, Kasshim Shettima bisa yin “aiki tukuru” wajen farfado da kuma ginin cigaba jihar ta Borno.
Shima a nashi bangaren, Shehun Borno, Alhaji Abubaka Ibn Garbai El-Kanemi, yayi kira da gwamnatin tarayya data saka ‘ya yan jihar Borno a cikin wasu daga mukaman gwamnati da gwamnatin zata bayar domin su sake gina garin na Borno da Boko Haram tayiwa ta’adi.
