Bamu hana Almajiranci yanzu ba, sai dai muna da muradin haramtawa a nan gaba – Buhari

Karatun minti 1

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyanawa cewa har zuwa yanzu gwamnatin bata kai ga haramta tsarin karatun almajiranci ba, sai dai akwai muradin haramtawa anan gaba.

Shugaba Buhari ya bayyana haka a wata sanarwar mai dauke da sa hannun Mallam Garba Shehu, inda yace yayi maganar ne bisa yadda wasu kafafen yada labarai suke rawaita cewa gwamnatin ta haramta shirin a halin yanzu.

“Soke tsarin Almajirci (Neman karatun Al-qur’ani wanda ya hadu da bara da neman kudi wanda ya zama ruwan dare a wasu jihohin Arewa) yana daga cikin abinda muka saka a gaba, amma gwamnatin shugaba Buhari bata haramtashi a yanzu ba.”

DABO FM ta tattaro cewa sanarwar tace akwai wasu kafafen yada labarai da suka fitar da rahoto cewa gwamnatin ta haramta shirin Almajiranci.

Sai dai Mallam Garba Shehu yace gwamnatin sam bata kai ga hana shirin yanzu ba amma tana kan hanya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog