Ban karbi Sarautar Bichi don rage darajar Sarki Sunusi ba – Aminu Ado Bayero

dakikun karantawa
Sarkin Kano - Alhaji Aminu Ado Bayero

Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero yace bai karbi sarautar Bichi da zummar cin mutunci ko ragewar sarautar Sarki Sunusi daraja ba.

Sarkin ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai inda bayyana karbar sarautar ba a matsayin mataki na cin mutunci Muhammadu Sunusi II ba.

Yace yakamata mutane su gane cewa komai yana iya chanzawa a kowana irin lokaci.

“Tin shekarar 1963 da mahaifina ya zama Sarkin Kano, abubuwa sukayi ta chanzawa, kuma zasu cigaba da chanzawa.”

“Bari na baku wani misali; mahaifina ya nada ni sarautar Dan Majen Kano a 1990, daga baya na koma Danburan Kano daga nan na zama Turakin Kano, bayan nan na zama Sarkin Tsakar har daga karshe dai na zama Wamban Kano.”

“Ban taba rokar ko daya daga cikin wadanda mukaman ba.”

“Daga lokacin da mahaifina ya zama Sarki har zuwa mutuwarshi, ya ga sauya-sauya irin daban-daban, kuma dukkaninsu ya karba hannu bibbiyu.

“Iyayenmu da kakanni sun karbi sauyin da ya karbe ikon masarauta akan ‘Yan doka, ‘Masu kula da fasakauri ta kasa, Alkalai da Makarantu.”

“A gani na, samun sarakuna 5 a jihar Kano bazai kawo cikas ga cigaban jihar ba. Idan har sarakan zasu saka bukatar mutanensu a gaba, su hadu hannu da karfe, to babu shakka zasu samarwa da jihar cigaba. Babu wani bambamci tsakanin mu.

Sarkin Bichi, Alhaji Bayero ya kara tsokaci akan dangantakarshi da Sarkin Kano, Muhammdu Sunusi II, inda ya bayyana babu wata matsala tsakaninsu.

“Sunusi dan uwa na ne, muna girmama juna. Ni dan Sarauta ne, ina daya daga cikin farkon wadanda suka fara masa mubaya’a lokacin da ya zama Sarkin Kano.”

“Babu abinda zai sauya a tsakanina da shi, dan nazama Sarki, nasan bazai ki bani duk wata gudun mawa domin inyi abinda ya dace ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog