Labarai

Kyari ya yi biris da umarnin Buhari na cire wasu Jakadun Najeriya a kasashen waje

Wani rahoto da Jaridar Sahara ta fitar yace daga ciki jakadun da Najeriya ta tura kasashen waje, akwai wadanda wa’adin aikinsu ya kare amma sun cigaba da aiki tare da karbe albashi da alawus da makudan kudade wanda hakan ya sabawa doka.

Itama a nata bangaren, sashin Hausa na Legit.ng ta rawaito cewa, wasu majiyoyin daga fadar gwamnatin tarayyace tace Mallam Abba Kyari, shugaban ma’ai fadar gwamnatin ne yayi watsi da umarnin da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na dakatar da jakadun daga aikinsu.

Ga cikakken rahotan daga Sashin Hausa na Legit.ng

“Jaridar ta ce akwai akalla Jakadu 25 na Najeriya da ya kamata a ce sun yi ritaya tun a tsakiyar shekarar 2018, sai dai har yanzu sun yi kememe sun cigaba da zama a ofis su na karbar albashi da alawus.

Daga cikin Jakadun kasashen da ya kamata a ce sun dawo gida akwai Jakadun Morocco, Kamaru, Kuba, Austriya, Kenya, Beljika, Mali, Indonesiya, Filifins, Sanagal, Hungary, da na Jamhuriyyar Czech.

Akwai Jakadun Najeriya masu uwa a gidin-murhu da su ke rike da mukaman na su duk da sun isa shekaru 60 a Duniya ko kuma sun yi akalla shekaru 35 su na aiki a dalilin kusanci da Malam Abba Kyari.

A Disamban 2018, Ministan harkokin wajen Najeriya a lokacin, Geoffrey Onyeama, ya gana da shugaban kasa Buhari a game da yi wa Jakadun kasar ritaya, kuma ya samu amincewar shugaban kasar.

Daga baya Ministan ya aika takarda a madadin shugaban kasa Buhari ga wadannan Jakadu su ajiye aiki. Daga baya babban Hadimin shugaban kasa, Abba Kyari ya kyale wadannan Jakadu na-kusa shi a ofis.

Rahotannin sun nuna cewa babban dalilin da ya sa a ka bar wadannan Jakadu da wasu sababbi da aka nada a bakin aiki shi ne kusancin su da COS Abba Kyari da kuma shugaban NIA na kasa.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin tarayya zata fara rabawa ‘yan Zamfara N5000 a kowanne wata – CCT

Dabo Online

Zamu fara amfani da gogewar mu ta yakin Basasa domin fatattakar Boko Haram -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Ku haramta kungiyar Shi’a – Kotu ta umarci gwamnatin tarayya

Dabo Online

El-Rufa’i yayi tir da kashe Tiriliyan 17 a gyaran wutar lantarki da gwamnatin Buhari tayi

Muhammad Isma’il Makama

Ba ƙaramin namijin ƙoƙari nake wajen mulkar Najeriya ba tare da ta wargaje ba -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Ƙurunƙus: Buhari ya hana ministoci zuwa yawon gantali ƙasashen waje

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2