Najeriya Nishadi

Barayin Kannywood: Sun sace miliyan 23 – Ummi Zee-Zee

Sani Danja, Fati Muhd, Zahraddin Sani, Al-amin Buhari da mai bada umarni Eemrana, sune manyan barayin Kannywood a cewar Ummi Zee-Zee.

Bayanan data wallafa a shafinta na instagram, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zee-Zee tace dan takakar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya shirya wani taro da zaiyi da mawaka da kuma ‘yan wasan kwaikayo masu ra’ayin jami’iyyar PDP a masana’antar Kannywood dangane da siyasarshi.

Taron da ya samu wakilicin shugaban majalissar dattawan, Alhaji Abubakar Bukoula Saraki wanda aka gudanar a ranar juma’ar data gabata.

Ummi Zee-Zee ta kara da cewa an basu miliyoyi makudai domin suyi amfani dashi wajen yakin neman zaben da sukeyi na tabbatar da samun nasara a zaben da za’a gudanar a watan Fabarairun shekarar 2019.

Jarumawan sun raba kudin ne a tsakaninsu ba tare da sun bawa kowa ba, wanda ya kai ga kowanne su samun kudi kimanin naira miliyan hudu da rabi. Ta nemi a bata nata kason, domin kudi ne na kowa, an tura mata naira dubu ashirhin da biyar ta hannun Zahraddin Sani Owner a cewar Ummi Zee-Zee.

Tayi gargadi da kuma ikirarin kai su gaban hukumar DSS a duk sanda irin wannan al’amarin ya sake faruwa.

Jaruma Sani Danja, fitaccen jarumi ne a masana’antar Kannywood wanda kowa ya sanshi da ido a acikin tafiyar jam’iyyar PDP tin lokacin gwamnatin data shude ta shugaba Goodluck Jonathan.

Zaharaddin Sani Owner, shima fitaccen jaruma ne da a iya cewa a wannan kakar aka fara ganinshi a cikin hidundumin siyasar, inda shima ya dau layin yiwa PDP yakin neman zabe.

Kungiyar Kannywood din dai ta rabe kashi biyu, kowa ya dau layinshi a siyasance, irinsu jarumi Ali Nuhu, Adam A. Zango da Nazir M. Ahmad duk yan yatiyar APC ne, yayinda Sani Danja, Shariff Momo da Abba El-Mustapha ‘yan tafiyar PDP ne.

Ni nafi karfin wannan kudin amma na kasa suma yakamata ace sunsan abinda akeyi

 

Daga shafin UmmiZeeZEE
Daga shafin UmmiZeeZEE
Daga shafin UmmiZeeZEE
Daga shafin UmmiZeeZEE

Karin Labarai

Masu Alaka

Darakta Hassan Giggs zai dauki nauyin yi wa wani matashi tiyatar ido

Dabo Online

Gobara a Kannywood: Mun sasanta da Mustapha Nabruska – Hadiza Gabon

Dabo Online

Maryam Booth za ta raba buhuhunan Shinkafa, Mai da sauran kayayyakin abinci

Dabo Online

Kura ta Lafa: Manyan Kannywood sun sasanta Ali Nuhu da Adam Zango

Dangalan Muhammad Aliyu

KANNYWOOD: Amina Amal ta maka Hadiza Gabon Kotu bisa tuhumar cin zarafi

Dangalan Muhammad Aliyu

Yadda jaruman Kannywood suke taimaka wa yaduwar labaran bogi

Dabo Online
UA-131299779-2