Bauchi: Bala Muhammad na PDP ya lashe zaben Gwamna a jihar Bauchi

Dan takarar Gwamna a inuwar jami’iyyar PDP, Bala Muhammad, ya lashe zaben Gwamna a jihar Bauchin Najeriya.

Hukumar zabe ta bayyana Bala a matsayin wanda ya lashe zaben biyo bayan gama tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da aka sake yi a ranar Asabar din data gabata.

Sanata Bala Muhammad ya samu kuri’u kimanin 515,113 wanda hakan yasa ya kada Gwamna mai ci, wanda ya samu 500,625.

TALLA

Karamar hukumar Tafawa Balewa ce dai ta kawo tsaiko a fadar sakamakon jihar ta Bauchi inda hukumar ta INEC tace ta soke sakamakon karamar hukumar bisa wasu dalilai.

Bayan sake zaben a Tafawa Balewa dai, jami’iyyar PDP ta samu kuri’ai 39,225 yayinda APC ta samu 30,055.

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.

%d bloggers like this: