KANO: 4+4 da Sabon Sarkin Kano?

A dai dai lokacin da gwamnatin Kano take murnar lashe zaben da tayi, alkaluman wasu daga cikin jagororin tafiyar gwamnatin na nuna yunkuri wajen goyawa gwamna Ganduje baya domin cirewa ko dakatar da Sarki Muhammad Sunusi II.

A jiya an hangi wasu magoya bayan gwamnatin Kano, lokacin da suke murna a babban dakin taro na “Coronation Hall” dake cikin gidan gwamnatin Kano, sun hau cire hotunan mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sunusi II, dake cikin dakin taron.

Tin kafin a gudanar da zaben cike gurbi na 23/03/19, magoya bayan gwamnatin ta Kano suke ganin Sarkin yana goyawa bangaren Kwankwasiyya baya a zaben Gwamna, har ma takai ga suna cewa, “Jar Hula ce kawai ta rage wa Sarki.”

Masu Alaƙa  Mahaifin Kakakin Majalissar Jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ya rasu

Sai dai lamuran sukan iya kasancewa masu wahala, domin mafiya yawa cire Sarki musamman na Kano, yana bukatar goyon bayan gwamnatin tarayya.

Duk da ‘yan PDP suna ganin cewa Gwamnatin tarayya ta bada gudunmawa akan irin abinda ya faru a jihar Kano.

A jiyan dai hukumar INEC ta bayyana gwamna Ganduje akan wanda ya lashe zaben da aka gudanar na jihar Kano, da yawan kuri’u kimanin 9000.

Dai dai lokacin da ake cire hoton Sarki a fadar Gwamnatin Kano

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: