Ba za mu kara lamuntar malaman da basu cancanci koyarwa ba – Zulum

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum zai tantance malaman makarantun firamare matakin farko.

Babagana Zulum ya bayyana haka ne a yayin zama da ya gudanar da mahukunta kan sha’anin ilimi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wakilin DABO FM na jihar Borno, Ibrahim Mustapha ya shaida cewa gwamna ya tabbatar da cewar, gwamnatin jihar ba za ta lamunci cigaba da aikin malaman da basu cancanci koyarwa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzu, malamai da dama za suyi ta ayyukansu domin wata majiya ta bayyanawa manema labarai cewa gwamnatin za ta sallamesu tare da neman wandanda zasu maye gurbinsu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog