(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Sarkin Kano Sunusi II ya zama shugaban jami’ar gwamnatin jihar Ekiti

Karatun minti 1
Muhammadu Sunusi II
Muhammadu Sunusi II

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, ya zama shugaban jami’ar gwamnatin jihar Ekiti.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ‘NAN’ ya rawaito cewa Darakta labarai da kula kula da harkokin makarantar, Mr Bode Olafinmuagun, ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Sai dai NAN ta rawaito cewa bai bayarda cikakken bayanin ba kamar yada jaridar Daily Trust ta rawaito.

Mai martaba Muhammadu Sunusi II, ya maye gurbin Sarkin Ekiti, Oba Adegoke Olu Adeyemi, wanda ya shafe tsawon shekaru 4 a matsayin shugaban jami’ar a karkashin mulkin tsohon gwamnan jihar Ayo Fayose.

Sarkin Kano ya karbi aikin ta hannun matawallen Kano, Alhaji Ibrahim Ahmad.

Daga karshe, mai martaba ya nuna godiyarshi ga gwamnan jihar, Kayode Fayemi tare da daukacin gwamnatin jihar Ekiti bisa karramawar da sukayi masa na bashi shugabancin makarantar.

Ya kuma alkauranta yin amfani da kwarewarshi wajen tabbatar da ciyar da jami’ar gaba.

DABO FM ta binciko cewa a yanzu haka Mai martaba sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sunusi II, yana shugabantar jami’o’i 4 a tarayyar Najeriya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog