Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

EFCC ta damke wani Kansila a Kaduna da laifin lamushe naira Miliyan 11

1 min read

Hukumar yaki da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta tasa keyar wani kansila a garin Kaduna mai suna Theophilus Madami a kan tuhumarsa da laifin karkatar da makudan kudi naira miliyan 11.

Hukumar Efcc ta wallafa haka ne a shafukan ta na kafar sadarwar yanar gizo, inda tace Madami shi ne kansilan dake wakiltar mazabar Kakuri Hausa a karamar hukumar Kaduna ta kudu.

EFCC ta ce ta kama Madami ne a kan zarginsa da zamba cikin aminci da kuma bindiga da kudi naira 11,080,000 bayan wani mutumi mai suna Ibrahim Ringima Haruna, shugaban kamfanin Pyramid Supplied Services Limited ya shigar da kararsa.

A watan Nuwambar shekarar 2018 ne kamfanin Ringim suka sayar masa kaya na naira 16,080,000, bayan ya basu kudin kafin alkalamin naira miliyan 5, amma daga nan bai sake biyan cikon ba, sa’annan ya cinye kayan.

Daga karshe hukumar tace za ta gurfanar da Madami gaban kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike a kansa.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.