(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
/

‘Yan daba sun kashe ma’aiktan INEC biyu, sun kone motoci a Akwai Ibom

Karatun minti 1

Yan daba sun kashe ma’aiktan INEC biyu, sun kone motoci 2 a Akwai Ibom.

Wasu bata gari da ake zargin ‘yan daban siyasa ne, sun kai farmaki wani ofishin hukumar zabe ta INEC hari a jihar Akwai Ibom.

An samu rahotan mutuwar mutum biyu tare da kona motoci masu yawa kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya rawaito.

‘Yan daban sunyi yunkurin sace kayayyakin zaben da aka ajiye a ofishin hukumar dake karamar hukumar Obot-Akara biyo bayan dage zaben da hukumar INEC tayi zuwa 23 ga watan Fabarairu.

Kwamishinan hukumar zabe na shiyar Jihar Akwa Ibom, Mr Mike Igini ya tabbatar da faruwar al’amarin kamar yadda kamfanin dillancin larabai na NAN ya rawaito.

Sai dai har yanzu hukumomin tsaro basu ce komai akan lamarin ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog