Home LabaraiBola Tinubu ya bada tabbacin sakin ‘Yan Arewa 123 da aka tsare a Legas

Bola Tinubu ya bada tabbacin sakin ‘Yan Arewa 123 da aka tsare a Legas

by Dabo Online
0 comments

Uba a jami’iyyar APC da jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da tabbacin sakin ‘yan Arewa 123 da gwamnatin jihar Legas ta tsare bayan shigowarsu jihar a cikin babbar Mota.

DABO FM ta tabbatar da Gwamnan jihar, Badaru Abubakar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da sakataren gwamnan, Auwalu D Sankara ya fitar yayin martani da tsare ‘yan jihar Jigawa a jihar Legas.

“Bayan mun tuntubi jami’an gwamnatin jihar Legas, Gwamna Badaru, wanda baya kasar a yanzu haka, yayi magana Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya tabbatar da za’a saki mutanen da gwamnatin take tsare da su.”

Ranar Juma’a ne dai gwamnatin jihar Legas, a shafinta na Twitter, ta tabbatar da tsare ‘yan Arewa 123 wadanda suka shigo jihar daga sassa daban-daban na jihohin Arewacin Najeriya.

Hukumar tace bata kama mutanen da wani haramtaccen kaya ko makami ba, illa iyaka mutane 48 daga cikinsu sun shigo da babura domin yin sana’ar Kabu-Kabu.

Sai dai an bayyana tsare ‘yan Arewa a matsayin wani yunkuri na wulakanta mutanen Arewa domin babu wata doka da ta hana dukkanin wani ‘dan Najeriya zuwa kowacce jiha a cikin Kasar.

Babu wata doka a Najeriya da ta hana mutane suyi sana’ar da zasu samu kudaden shiga indai bata sabawa doka ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00