Home Labarai‘Yan Najeriya su cire Rai da samun tsaro a gwamnatin Buhari – Mungadi

‘Yan Najeriya su cire Rai da samun tsaro a gwamnatin Buhari – Mungadi

by Dabo Online
0 comments

Alhaji Shu’aibu Yusuf Mungadi, ma’aikaci a kamfanin Labarai na Vision Abuja yace; “‘Yan Najeriya su cire Rai da samun tsaro a gwamnatin Buhari”

DABO FM ta binciko cewa; Babban ma’aikacin gidan labaran ya bayyana haka a yayin wata ganawarshi a shirin Idon Mikiya da ake gabatarwa a tashar Farin Wata TV.

Ya kara da cewa dukkanin masana sha’anin tsaro sun tabbatar da hakan bisa dalilin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya “Ba ta ma yarda cewa matsalar tsaron takai intaha kamar yacce take a yanzu ba.”

Ya kara da cewa dukkanin masana sha’anin tsaro sun tabbatar da hakan bisa dalilin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya “Ba ta ma yarda cewa matsalar tsaron takai intaha kamar yacce take a yanzu ba.”

Alhaji Mungadi ya alakanta rashin tsaron da abubuwa wandanda suka hada da;

“Rashin gasgata zargin hannun Jami’an tsaro cikin tabarbarewarshi a kasa.”

Fitar da labaran karya da hukumomin tsaro sukeyi har ma ya bada labari akan bayanan da ‘yan sanda suka fitar na cewa “Su sune suka kubutar da daliban ABU Zaria guda 3, alhalin dangin daliban su karyata.”

DABO FM ta binciko; a karshen hirar, Alhaji Mungadi ya bayyana cewa; “Zancen yaki da wannan al’amari (Rashin Tsaro), babu shi, karyayyki ne da yaudara suka shiga ciki.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00