Bola Tinubu ya kira Obasanjo da lalataciyyar madara

Karatun minti 1

Bola Ahmed Tinubu, ya zargi tsohon shugaban kasar Najeriya dayin magudin zabe a shekarar 2003 da 2007.

Tinubu, yayi kira ga ‘yan Najeriya dasu kauracewa duk wata magana da Obasanjo zai fada, domin magana ce wacce take ba sahihiya ba kuma ya kirashi da wanda ya fara kirkirar magudin zabe a jamhuriya ta biyu a Najeriya.

A jawabin da yayi a taron yakin neman zaben Shugaba Buhari  da aka gudanar yau a jihar Lagos, ya kara da cewa (Tinubu), lokacin da Obasanjo yake mulki, ya kori kamfanin taya na Michelin, kamfanin Dunlop da kuma kamfanin Siemens. So sukeyi mu kara zabarsu domin su cigaba da kai kudinmu kasashen Turai.”

Mahalarta da ya samu halartar shugaban kasa Muhammad Buhari, Gwamna Ambode na jihar Legas, shugaban jami’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomole dama sauran gwamnoni da wasu ‘yan jami’iyyar adawa masu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog