(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Buhari ya hana Atiku wajen taro a Abuja

Karatun minti 1

A lokacin da bai wuce kasa da sati daya a gudanar da babban zaben kasar Najeriya ba, gwamanatin Shugaba Muhammadu Buhari ta hana ‘dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jami’iyyar, Atiku Abubakar filin taro na Old Parade Ground dake birnin Abuja.

PDP ta zargi gwamnatin APC da yin zambo cikin aminci bayan da PDP tace sun gama biyan kudin kama hayar wajen taron amma daga bisani gwamanatin ta ce bazasu gudanar da taro a filin ba.

Da yake bayani, shugaban shashin sadarwa da mu’amalar mutane na jami’iyyar PDP, Mr Kola Ologbondiyan yace sun biya duk wani kudi da ake biya domin hayar filin da zasu gudanar da taro ranar asabar, amma daga bisani aka kirasu domin su karbi kudin hayar filin da suka riga suka bayar.

Dokar tazo daga sama ne kuma babu yacce kuma iya, a cewar masu kula da filin Old Parade Ground.

APC, Buhari bazasu hanamu gudanar da taronmu kamar yadda muka shirya ba, acikin birnin Abuja. Babu gudu babu ja da baya. – PDP

Karin Labarai

Sabbi daga Blog