Labarai

Budurwa ta caccakawa Saurayinta na daduro wuka a jihar Legas

An zargi Stella Peters, da caccakwa saurayinta na daduro wuka har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa; Budurwar ta caccakawa Saurayin wuka bisa rashin bata kudin hidumar murnar zagayowar ranar haihuwar diyar da suka haifa.

Sai dai tin a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, rudunar ‘yan sandan jihar Legas ta hannin kakakinta, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da kama budurwar da ake zargi.

Ya bayyana cewa suna zaune ne a a gida mai Lamba 2 dake unguwar Surulere na tsawon shekaru 3 tare da ‘yar da suka haifa mai shekara 1.

Ya kara da cewa bayan bincike, sun gano cewa masoyan basu da shaidar data tabbatar da su ma’aurata ne.

Tini dai saurayin, Haruna Bala, ya rigamu gidan gaskiya sakamakon sukar da ya sha a wajen budurwar mai shekaru 23 a duniya.

Sako na musammann

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

Comment here