El Rufa’i
Labarai

El- Rufa’i zaiyi sabuwar dokar hana Likitocin Gwamnati aiki a asibitoci masu zaman kansu

Gwamnar jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce, nan bada dadewa ba gwamnatinsa zata samar da wata doka da zata haramtawa likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnatin jihar budewa ko yin aiki a asibitoci masu zaman kansu a jihar.

Dabo FM ta tattaro gwamnan ya ce; duk wanda yaga ba zai bi wannan doka ba toh yana iya ajiye aikinsa ya je ya bude asibitin nasa.

DABO FM ta binciko gwamnan yana bayyana shirin sabuwar dokar a lokacin da yake amsa tambayoyi a wata tattaunawa da yayi da manema labarai wanda aka saka a gidajen radiyoyin jihar kai tsaye a karshen makon nan.

A cewar Gwamnan, dole ne likitocin da ke aiki asibitin gwamnati su zabi daya in ma dai ci gaba da aiki a asibitin gwamnati ko kuma a asibiti mai zaman kansa.

Ya kara jaddada cewa, za su kira likitocin a sanar da su cewa duk wanda ya bude asibiti mai zaman kansa dole ya rufe in kuma ya zaba yin aiki asibitinsa ne toh sai ya bar aiki.

“Muna da labarin yadda mutane marasa lafiya ke zuwa asibitin gwamnati domin neman magani amma sai irin wadannan likitoci su fada masu cewa cutarsu ba tanan bane dan haka sai su turasu nasu asibitin wanda yin hakan ba daidai bane cin amana ne”. In ji shi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin Kaduna ta shirya yiwa Dawakai 1000 allular rigakafin kamuwa daga Zazzabin Dabbobi

Dabo Online

Yarjejeniyar yin kamfanin Madara tsakanin Kaduna da Denmark zai samar da ayyukan yi 50,000

Dabo Online

Babban shehin malamin coci ya samu wahayin El-Rufa’i bazai taba mulkin Najeriya ba

Muhammad Isma’il Makama

An sace fiye da mutane 60 a Kaduna, mutum 6000 na kan hanyar gudun hijira a jihar

Muhammad Isma’il Makama

Hanyar Kaduna zuwa Abuja tafi kowacce hanya tsaro a duk fadin Najeriya -El Rufai

Muhammad Isma’il Makama

Kaduna: Rusau da gwamna El-Rufa’i zai yi a kasuwar Sabon Gari bazata shafi ‘Yan Kasuwa ba

Mu’azu A. Albarkawa
UA-131299779-2